Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola ta Fice Daga Najeriya Inji Hukumar Lafiya ta Duniya


Hukumar lafiya da Duniya a yau litini ta bayana Najeriya, a matsayin kasar da ta fice daga barazanar cutar Ebola, kwanaki 42, bayan da aka yiwa mutunin karshe da ya kamu da cutar magani, batare da samu wani mai dauke da cutar ba, a kasar.

Da take bayana wannan nasaran da Najeriya, ta samu jami’ar hukumar lafiya ta duniya, Rui Gama Vaz, ta ce . a yanzu cutar ya bace. Ta kara da cewa Najeriya ta kau da annobar daga kasar, tyana mai cewa Najeriuya tayi rawar gani.

Ministan, kiwon lafiya na Najeriya, Dr. Haliru Alhassan, ya bayana wannan nasaran da cewa nasara ce da kasar baki daya ta samu saboda kyakayawan hadin kai ta fahimtan juna.

Ya kara da cewa har yanzu akwai sauran aiki, da fatan jama'a zasu ci gaba da kiyaye cin namomin daji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG