Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya za ta Ziyarci Cibiyar Barkewar Cutar Ebola.


Ebola
Ebola

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Samantha Power za ta ziyarci wuraren da su ne cibiyar barkewar cutar Ebola.

Samantha Power za ta ziyarci kasar Guinea da Laberiya da kuma Saliyo. Ta shaidawa manema labarai a jiya Asabar cewa zuwa da kan ta ta ganewa idanun ta halin da ake ciki a kasashen ya fi.

Samantha Power za ta ziyarci cibiyoyin tsara dabarun yaki da Ebola, kuma ta gana da jami'an gwamnatocin kasashen, da kwararrun likitocin Amurka da sojojin kasar masu yaki da cutar.

Kasashen Guinea da Laberiya da Saliyo su na cikin dabaibaiyin matsalar cutar Ebola wadda ta hallaka mutane fiye da dubu 5 daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da ita su fiye da dubu 10. Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce a gaskiya yawan na iya fin haka saboda iyalai da dama sun yi kokarin jinyar masu fama da cutar a gida.

Haka kuma a jiya Asabar Majalisar Dinkin Duniya, ta tura kayan agajin gaggawa mai nauyin ton daya wato kilogram dubu daya zuwa kasar Mali bayan ta bada labarin mutuwar mutum na farko a kasar sanadiyar cutar Ebola.

Wata yarinya 'yar shekaru biyu da haihuwa ce ta mutu ran Jumma'a a kasar ta Mali bayan fitowar su daga kasar Guinea.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta bas yarinyar da iyayen ta suka je Mali, saboda haka watakila cutar ta harbi wasu mutane a kasar ta Mali.

A halin da ake ciki kuma, gwamnan jahar Illinois Pat Quinn ya bada umarnin daukan matakin sanya duk wanda ya je jahar daga Guinea ko Laberiya ko Saliyo, cikin zaman kullen dole na kwanaki 21a killace. Umarnin ya shafi duk wanda yayi mu'amala kai tsaye da mai cutar Ebola.

XS
SM
MD
LG