Kasashen Afirka Na Shirin Shiga Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Zauren taron kungiyar Tarayyar Afirka ta AU a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar

Afrika tana shirin shiga wata yarjejeniyar da ta kira ta zaman lafiya da ci gaba ta hanyar kulla yarjejeniyar kasuwanci a nahiyar a hukumance.

Kasar Nijeriya ita ce mafi karfin tattalin arziki a Afrika ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da Benin a jiya Lahadi a wurin taron kolin Tarayyar Afrika a Nijer. Eritrea itace kadai kasar da ta rage da bata shiga wannan yarjejeniyar ba.

Masanan sun ce an samu nasara kana sun yi hasashe tara dala tiriliyan uku da biliyan dari hudu a wannan yarjejeniyar kasuwanci wacce zata kai ga samar da ayyukan yi da ci gaba.

Wannan nasara ce ga cimma daddadiyar manufa, wadanda suka hassasa wannan tafiya zasu yi alfahari, inji shugaban hukumar zartarwar kungiyar Taryyar Afrika Moussa Faki a jiya Lahadi, yayin da shugaban kungiyar kuma shugaban Misra Abdel Fattah al-Sisi ya fada cewa nasara kulla yarjejeniyar kasuwancin zata zama zakarar gwajin dafi wurin cimma bunkasar tattalin arziki, lamarin da zai kai ga kyautata rayuwar mutanenmu.

An kwashe shekaru 17 wurin tattaunawa mai wahala kafin cimma babbar yarjejeniyar a jiya Lahadi, abin da masana ke cewa zai bunkasa harkokin kasuwanci a kasashen Afrika ta kashi 60 cikin dari a cikin shekaru uku.