Kasashe Dake NATO Sun ce Babu Fashi Kan Matakan Soji A Libya Har Sai....

Hayaki ya tashi bayan da jiragen NATO suka gilma ta cikin birnin Tripoli.

Shugabannin Ingila Faransa da Amurka sun ce kungiyar tsaro ta NATO zata ci gaba da matakan soji da take dauka a Libya har sai Moammar Gadhafi ya bar mulki.

Shugabannin Ingila Faransa da Amurka sun ce kungiyar tsaro ta NATO zata ci gaba da matakan soji da take dauka a Libya har sai Moammar Gadhafi ya bar mulki,a dai dai lokacinda ‘yan tawaye suke bada labarin harin da dakarun Libnya suka kai birnin Misrata da aka yi wa kawanya ya kashe mutane 23.

A cikin kasidu da shugabannin uku suka wallafa a manyan jaridun kasashen yau jumma’a, sun ce zai kasance rashin tunani a ce mutuminda yayi kokarin halaka jama’arsa,san nan ace yana da hanu wajen shata makomar mulkin kasar nan gaba.

Duk da haka Gadhafi bai nuna alamar yana shirin mika wuya ba,saboda dakarunsa sun yi luguden wuta kan birnin Misrata da nufin lalata tashar ruwa dake birnin, kafarda ‘yan tawaye suke da ita wajen mu’amala da ketare.

Ahalin yanzu kuma tashar talabijin ta Libya, ta bada labarin harin jiragen NATO kan birnin Tripoli.

Duk da harin, tashar talabijin din ta nuna shugaba Moammar Gadhafi yana cikin wata budaddiyar mota kan titunann birnin,yana daga hanu yana gaida mutane.