A wannan ranar dai hukumomi da masana na taruka domin gano bakin warware matsalar abinci a duniya, Najeriya na daya daga cikin kasashe masu tasowa da al'umarta ke fuskantar barazanar yunwa musamman a yankin kudu maso gabashin kasar.
Maudu’in taron na wannan shekarar shine kawo karshen yunwa kwata-kwata a duniya, kuma fatan hukumar abinci shine kawo karshen yunwa kafin nan da shekaru 15, masu zuwa.
Kasashe da dama ciki harda Najeriya, sun bayyana aniyarsu ta rungumar noma gadan-gadan lamarin da aka tabbatar zai taimaka wajan inganta rayuwa da kuma kawar da talauci a tsakanin al’umma.
Sai dai kuma masana ilimin kimiyya na ganin cewa hanyar da za a iya bi wajan kawar da yunwa tsakanin al’umma ita ce, wajan tsarrai, lamarin da zai haifar da abinci mai yawa ga mutanen da yanzu haka ke fama da rashin isashshen abinci a sassa daban daban na duniya.
Dr Abdul’razaq Ibrahim, malami a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma daya daga cikin masu gudanar da bincike a cibiyar binciken harkokin noma dake nazari kan samar da abinci ta hukumar Ecowas dake kasar Ghana, ya bayyana cewa yawan bincike ya bayyana cewa yawan jama’a zai karu dan haka daya daga cikin hanyoyin da za a iya inganta harkokin noma sai an yi amfani da fasahar zamani.
Kuduirn kawar da yunwa a cewar hukumar zai taimaka wajan ceto rayukan yara da kuma samar da ingantacciyar lafiya ga mata masu juna biyu da kuma garkuwa ga kananan yara da ake haihuwa.
wakilinmu babangida jibrin ya aiko mana da karin bayani daga Legas.
Your browser doesn’t support HTML5