Kasashe 32 Ne Zasu Fafata A Gasar Cin Kofin Duniya

FIFA President Gianni Infantino speaks during a news conference at the St. Petersburg Stadium, Russia, July 1, 2017. Chile lost to Germany in the Confederations Cup final.

A shirye shiryen gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a buga a kasar Rasha kuwa tuni aka kasa kasashen talatin da biyu (32) da zasu fafata a gasar zuwa gida hudu gabanin raba su zuwa rukuni rukuni da zasu kasance a lokacin buga gasar.

Ga yadda aka kasa kasashen Russia, Germany, Brazil, Portugal, Argentina, Belgium, Poland da France a kashin farko, inda kashi na biyu ya kunshi kasashen Spain; Peru, Switzerland, England, Colombia, Mexico, Uruguay da Croatia.

Kashi na uku nada kasashen Denmark, Iceland, Costa Rica, Sweden, Tunisia, Egypt, Senegal da Iran. Kashi na hudu kuwa ya kunshi Serbia, Nigeria, Australia, Japan, Morocco, Panama, Korea Republic da Saudi Arabia.