Tawagar Kungiyar kwallon kafar maza ta kasar Italiya ta gaza samun tikitin halartar shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na shekara 2018 da za'ayi a kasar Rasha.
Wannan shine karo na farko da kasar ta Italiya, ta yi rashin samun nasara na halartar shiga gasar tun shekara ta 1958 kimanin shekaru sittin da suka wuce.
Hakan ya faru ne sakamakon canjaras 0-0 da suka yi da kasar Sweden, a jiya litinin 13/11/2017 a wasansu na biyu da suka yi na neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya, inda a karawarsu ta farko, Sweden ta doke ta da kwallo 1-0.
A tarihin gasar ta cin kofin kwallon kafa na duniya tun 1930, Kasar Italiya ta lashe gasar sau hudu ta samu zama a matsayi na biyu (Runners-up) sau 2, mataki na uku sau daya, kuma wannan shine karo na biyu da kasar bata je gasar ba tun farawa da akayi a shekara ta1930.
Bayan tashi daga wasan, mai horas da kungiyar ta Kasar Italiya Venture dan shekaru 69 da haihuwa yaki cewa komai bisa tambayoyi da ‘yanjarida suka yi masa, wanda wasu ke hasashe cewar kocin zai yi ritaya a fannin horas da ‘yan wasa.
Shima mai tsaron raga na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Gianluigi Buffon, wanda shine jagoran ‘yan wasan kasar Italiya, ya bayyana ajiye takalman taka ledar da yake ma kasarsa ta Italiya.
Buffon, mai shekaru 39 da haihuwa ya zubda hawaye, ya kuma nuna bacin ransa bisa rashin halartar su gasar cin kofin kwallon kafa na duniya 2018, da za'ayi a Kasar Rasha.
Facebook Forum