A kasar Turkiyya tsadar kaya ta karu da kashi 18 cikin 100 a watan Agusta, tsadar da ya kamata a ce ta faru cikin shekaru 15, hakan kuwa ya biyo bayan faduwar darajar takardar kudin Turkiyya ta Lira, faduwar da ta kai kashi 20 cikin 100 cikin 'yan makonnin da su ka gabata.
WASHINGTON D.C. —
Karuwar tsadar kaya da kuma faduwar darajar kudi na janyo fargabar yiyuwar kasar ta Turkiyya na gab da faduwa cikin matsalar tattalin arziki.
A wani bayani a shafinsa na internet, Babban Bankin kasar Turkiyya, ya sha alwashin daukar matakan da su ka wajaba da kuma sake tsarin harkokin kudin kasar a taron da za a yi ranar 13 ga watan Satumba, lokacin da za a tattauna kan tsarin riba.
Alkaluman tsadar kaya na baya-bayan nan sun nuna cewa Lira ta dan farfado.