Kasar Somalia Zata Karbi Bakoncin Taron Kolin Cibiyoyin Raya Kasashen Afirka

Birnin Mogadishu

Babban birnin Somalia Mogadishu, wanda bada dadewa ba ake daukar shi a matsayin birni mafi hadari a duniya, yanzu yana shirin daukar bakwancin taron koli na Hukumar “IGAD” ta Cibiyoyin Raya Kasashen Afrika na 53 a karon farko, a karshen wannan mako biyo bayan yakin basasa da aka kwashe shekaru da dama ana kasar, inji jami’ai.

Shugabanni kasashen Djibouti, Ethiopia, Kenya, Somalia, Sudan ta Kudu, Sudan da Uganda zasu halarci taron wanda zai mai da hankali kan ci gaba siyasa da tsaro da aka samu a Somalia, da zancen zaben kasar mai zuwa a wannan shekara ta 2016 da kuma batun rikicin siyasar Sudan ta Kudu, a fadar jami’an diplomasiya.

A wata hira da yayi da Muryar Amurka, ministan harkokin waje Somalia Abdisalam Omer Hadliye yace wannan babban abin tarhi ne ga Somalia, da yake wannan shine karon farko da Somalia ke daukar nauyin irin wannan taron a cikin shekaru fiye da 30.

Ministan yace ba zai yanke tsammanin cewa za’a fuskanci kalubale na tsaro da kungiyar ta’adda ta al-Shabab ke yi a Somalia, da yake ta jima tana kawowa harkokin tsaron kasar cikas, da ma wasu mawabtan Somaliar musamman Kenya, kuma suna ci gaba da kai hare haren kunar bakin wake.

A makon da ya gabata ma, wani bam da ya tashi a wata mota, ya kashe mutane akalla 25 kusa da fadar shugaban Somalia.