Kasar Kenya Ta Fara Samar Da Ruwa Ga Al’ummomin Da Ba Su Da Shi A Zahiri Daga Iska

Kenya

Kamfanin Majik Water yana amfani da na’urar da aka kera a Indiya, wacce ke zakulo tururi daga iska ta amfani da matatar lantarki. Da wannan fasahar, ana iya samar da ruwa kimanin lita 500 a kowace rana a yankunan da ba su da ruwa.

WASHINGTON, D. C. - Samun ruwa mai tsafta yana da wahala ga mutanen da ke zaune a yankunan da ke fama da rashin ruwa. Saboda sauyin yanayi da kuma yawan fari, inda magudanun ruwa da koguna suke yawan bushewa, wanda hakan ke haifar da kalubale ga iyalai da ke kokarin rayuwa.

Wacce ta kafa, Beth Koigi, ta ce inginan janareton na iya samar da ruwa har lita dari 500 a rana.

Beth ta kuma ce “Lokacin rani na zama kusan ko yaushe, kuma manufar wannan tsarin dungurungum ita ce ba da dama ga al’ummomin su sami ruwan sha mai tsafta ba tare da dogaro ga hanyoyin samun ruwa na yau da kullum ba.

Don haka, a yankunan da, idan ruwan rijiyar burtsatse su ka shanye, kogunan wucin gadi su ka kafe, al’ummomin za su iya samun taftataccen ruwan sha.”