Wasu mambobi 7,000 na ma'aikatan kiwon lafiya a Kenya, da na kantin magunguna da kuma Ƙungiyar likitocin Haƙora sun yi tattaki a tsakiyar watan Maris don neman ingantaccen albashi da ingantaccen yanayin aiki.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, kotun da’ar ma’aikata a Nairobi ta dakatar da yajin aikin a watan da ya gabata. A ranar Laraba ne dai ta bayar da umarnin a kammala tattaunawar kawo karshen takun saka nan da kwanaki 14.
Matakin dai ya zo ne kwana guda bayan da gwamnatin kasar ta ce za ta biya wasu bukatun likitocin da suka hada da biyan basussukan da ake bi da kuma daukar likitocin da aka horar da su kwangiloli na dindindin.
Sai dai kungiyar ta bayyana rashin gamsuwarta da tayin - kuma ta ce gwamnati ta kawo karshen tattaunawar har sai an janye yajin aikin. Har ila yau, ta ce tayin da aka gabatar ba shi da alkawuran da suka dace da doka.
Kungiyar ta yi kira ga likitoci masu neman sanin makamar aiki wadanda ta ce su ne kusan kashi 30 na likitoci da kada su karbi wasikun kwangilarsu daga gwamnati.
Dandalin Mu Tattauna