Kasar Jamus ta ba 'yan tawayen kasar Libya rance

'Yan tawayen kasar Libya

Kasar Jamus zata ba majalisar ‘yan tawayen kasar Libya rancen dala miliyan dari da arba'in da hudu domin taimaka mata gudanar da ayyukan jinkai da sake gina kasar.

Kasar Jamus zata ba majalisar ‘yan tawayen kasar Libya rancen dala miliyan dari da arba'in da hudu domin taimaka mata gudanar da ayyukan jinkai da sake gina kasar. Ministan harkokin kasashen ketare na kasar jamus ya bayyana yau lahadi cewa, kasarshi zata bada rancen ne domin ba za a basu izinin amfani da kaddarorin shugaban kasar Moammar Gadhafi da aka hana shi tabawa ba a halin yanzu. Bisa ga cewarshi, bashin zai bada damar taimakon majalisar kungiyoyin hamayyar gudanar da muhimman ayyuka da kuma shawo kan karancin ababan jin dadin rayuwa. Wannan ya biyo bayan wani zama da aka yi cikin wannan watan a Turkiya, inda sama da kasashen 30 suka sanar da goyon bayan majalisar mika mulki ta ‘yan tawaye. A halin da ake ciki kuma kungiyar tsaro ta NATO ta kai harin sararin sama a Tripoli babban birnin kasar Libya. Shaidu sun ce, an sami a kalla fashewar nakiya daya kusa da gidan Mommahar Gadhafi yau da safe. Tashar talabijin ta kasar Libya ita ma ta laburta kai hare haren sararin sama a babban birnin kasar, sai dai bata bada karin haske ba. Babu rahoton wadanda hare haren suka shafa, Kungiyar tsaro ta NATO tace jiragen samanta sun kai hare hare kan sansanan sojojin kasar Libya ke Brega, da Al-Khum da kuma wadansu garuruwa kusa da Tripoli jiya asabar.