Yan tawayen kasar Libya sun ce sun isa garin Brega wani wuri mai muhimmanci cikin dare, bayan karfafa masu guiwa da kasashe da dama suka yi ta wajen amincewa halalcin majalisar mika mulki ta ‘yan yawaye a matsayin hukumar kasar dake arewacin Afrika. Yau asabar ‘yan tawayen suka shiga birnin mai arzikin mai suna kuma shirin kai hari wani lokaci yau. Sun bayyana asarar rayuka a arangamar da aka yi ta baya bayan nan. Ana ci gaba da gumurzu yayinda sama da kasashe 30, da suka hada da Amurka suka amince da sahihancin kungiyar TNC jiya jumma’a suka kuma bayyana shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi a matsayin haramtaccen shugaba. Shugabannin kasashen yammaci da kuma na yankin sun bayyana haka ne a Istanbul inda suke taron domin tsaida shawara kan matakan karawa ‘yan hamayyar kasar Libya karfi a yunkurinsu na hambare Mr. Gadhafi wanda ya shafe shekaru 42 bisa karagar mulki, Mr. Gadhafi ya yi wofinta muhimmancin samun goyon bayan diplomasiya a wani jawabi da yayi da aka yayatawa dubban magoya bayanshi a garin Zlitan.
Yan tawayen kasar Libya sun ce sun isa garin Brega wani wuri mai muhimmanci cikin dare, bayan karfafa masu guiwa da kasashe da dama suka yi ta wajen amincewa halalcin majalisar mika mulki ta ‘yan yawaye a matsayin hukumar kasar dake arewacin Afrika.