Kasar Chadi Na  Neman A Taimakawa Yankin Sahel 

Emmanuel Macron

Emmanuel Macron

Shugabanin G5 Sahel daga Burkina Faso , Chadi , Mali, Mauritaniya da kuma Nijar na halarta wannan taro na kwanki biyu a Ndjamena babban birnin kasar tare da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da ya halarshi taron ta hanyar yanar Gigo.


A jawabinsa na bude taron, shugaban kasar Chadi Idriss Deby Etino ya ce yankin Sahel na cikin halin kaka ni kayi lamarin da ya yi sanadiyar “talauci, wanda shine filin dasa akidar ta'addanci"

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby

Ya ce lokaci ya yi da kasashen duniya su gaggauta bada na su tallafin bunkasa yankin , da zai taimaka wajen toshe hanyoyin cusa akidar ta'addanci.

Wannan taron ya samu asali bayan da kasar Faransa ta kara yawan sojojinta a yankin domin kawo karshen wannan yaki da ya ki ci ya ki cinyewa.

Duk da yawan nasarori da sojoji suka samu, har ila yau ‘yan ta'adda na da nasara akan wasu yankuna da dama ,kuma suna ci gaba da kai hare hare.

Wasu sa'o i kalilan kafin abude taron, ofisoshin yada labarai kasar Mali yace wani bam ya kashe wasu sojoji biyu akan wata wani titi dake tsakiyar Mali.

Wannan kuma ya kawo yawan wadanda aka kashe a kasar Mali dake aiki da UN na dakarun kasar Faransa zuwa 29 a wannan sabuwar shekara ta 2021 a cewar kamfanin yada labarai na AFP.

Dakarun G5 Sahel

Dakarun G5 Sahel

A shekara 2017 kasashe biyar suka hada wata yarjejeniyar aika sojoji duba 5 amma shirin yana ci gaba a fuskantar kalubale na rishin kayan aiki , tallafi da kuma horo.

Kasar Chadi wadda ta ke da dakaru da suka fi kwarewa a tsakanin kasashen biyar ta yi alkawari shekarar da ta gabata na tura bataiya daya zuwa iyakoki uku na Mali , Nijar da kuma Burkina Faso. Amma har illa yau sojojin ba ta tura sokin ba su isa ba.


Gwaman kasar Faransa na fatar ganin nasarorin da aka samu a shekar da ta gabata za su iya karfafa yayanin siyasa a yankunan Sahel, inda rashin ingantacen jagoranci ya zamo sanadiyar tashe tashen hankula.