Karyewar Wata Gada A Wasu Kananan Hukumomin Jihar Jigawa Ya Dakatar Da Hada-hadar Yau Da Kullum

Karyewar Wata Gada A Wasu Kananan Hukumomin Jihar Jigawa Ya Dakatar Da Hada-hadar Yau Da Kullum

Harkokin tattalin arziki, cinikayya da zamantakewa na ci gaba da gurguncewa a sassan kananan hukumomin dake yankin kudancin Jihar Jigawa saboda karyewar gadojin dake kan titunan yankin biyo bayan ambaliyar ruwa.

JIGAWA, NIGERIA - Mamakon ruwan sama da ake samu akai-akai a daminar bana ya zo da kalubale ga manoma da magidanta dake rayuwa a birni da karkara, musamman a yankin arewacin Najeriya.

Jihar Jigawa na daya daga cikin jihohi na Arewa dake fuskantar wannan kalubale, inda yanzu haka ambaliyar ke ci gaba da lalata amfanin gona da rusa gidaje a garuruwa da kauyuka, baya ga lalata tituna da karya gadoji.

Fiye da mako guda aka kwashe ana cikin yanayin ba shiga ba fita a yankin karamar hukumar Birnin Kudu, biyo bayan karyewar gadojin dake kan hanyoyin da galibin matafiya daga Jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa, da-ma wani bangare na Jihar Borno zuwa Kano.

Karyewar Wata Gada A Wasu Kananan Hukumomin Jihar Jigawa Ya Dakatar Da Hada-hadar Yau Da Kullum

Wasu daga cikin al’ummar yankin da suka zanta da muryar Amurka sun roki gwamnatocin Jihar Jigawa da ta tarayyar Najeriya su kai musu dauki, la’akari da muhimmancin gadojojin ga harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Malam Isma’il Mustafa, wani mazaunin garin Birnin Kudu ya ce mutane daga garuruwa da kauyuka daga Jihohin makwafta ba sa iya ziyarta manyan asibitocin guda biyu, dake zaman kansu bayan bada harkokin kiwon lafiya ga jama’ar yankin.

Ku Duba Wannan Ma Daruruwan Gidaje Da Miliyoyin Naira Sun Salwanta Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Jihar Neja

Yanzu haka kimanin mutane 100 ne suka rasa rayukan su sanadiyyar hadduran kwale-kwale a sassan Jigawa, sai dai mataimakin gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya ce gwamnati na daukar matakan gyara gadojin da suka lalace, inda a hannu guda kuma suke kokarin samar da hanya ta wucin gadi domin baiwa jama’a damar ci gaba da zirga-zirgar yau da kullum.

Masu kula da lamura dai na ganin cewa, batun samar da injinan kwale-kwale na zamani da saka ido sosai kan yadda harkokin sufuri ke gudana a wuraren da gadojin suka karye na daga cikin al’amuran da hukumomin na Jigawa ya kamata su baiwa kulawar gaggawa, la’akari da yadda rayuwa bil’adama ke salwanta a gabar gadojin.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Karyewar Wata Gada A Wasu Kananan Hukumomin Jihar Jigawa Ya Dakatar Da Hada-hadar Yau Da Kullum.mp3