Kimanin kasa da mako guda bayan da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewar gwamnatinsa ta sauya ranar 29 ga watan Mayu da 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar bikin mulkin Demokiradiyya a Najeriya, da kuma baiwa Marigayi Cif MKO Abiola wanda ke ikirarin ya lashe zaben 12 ga watan yuni da Sojoji suka soke lamban yabo mafi girma a Kasar.
Har yanzu ‘yan Najeriya naci gaba da tofa albarkacin bakunan su game da cancanta ko rashin cancantar wannan mataki na gwamnatin. Akasarin ‘yan Najeriya na kallon wannan yunkurin a matsayin hanya da shugaban yabi don kawo kauna a tsakanin ‘yan kasar.
A bangare daya kuwa wasu na ganin hakan bai kamata ba, daya daga cikin masu irin wannan ra’ayin sun hada da Alh. Bashir Tofa, tsohon dan takarar jam’iyyar NRC, wanda yayi jayayya da marigayin MKO Abiola, yana ganin cewar ai ba’a kamala zaben ba don haka babu dalilin da zai sa a karrama shi domin kuwa ba zababben shugaban kasar bane.
Wani dan jarida kuma tsohon ma'iakacin jaridar Concode mallakar marigayi MKO Abiola, Muhammad Adamu, yana ganin hakan babbar nasarace ga siyasar Najeriya, domin kuwa duk wanda yayi duba da irin abun da ya faru a baya zai ga cewar hakan yayi dai-dai don zai kara hada kan ‘yan kasar musamman ‘yan kudu da na Arewa.
A gobe ne dai za’a karrama marigayin MKO Abiola, da Ambasada Baba Gana Kingibe, mataimakin na MKO Abiola, kana da marigayi Gani Fayomi, a goben dai idan Allah ya kai rai wasu daga cikin jihohin kudancin kasar sun sanar da cewar ranakun a matsayin ranakun hutu.
Saurari cikakken rahoton Babangida Jibril.
Your browser doesn’t support HTML5