A cikin wasu kalamai da ya yi ta kafewa a shafin Twitter, Trump ya ci gaba da wasu maganganu ba tare da gabatar da hujja ba, cewa an kayar da shi ne da magudi.
Shugaban, dan jam’iyyar Republican, ya ki amincewa da shan kaye a zaben a hukumance ga tsohon Mataimakin Shugaban kasar, duk da cewa duk manyan kungiyoyin yada labarai na Amurka sun ce tsawon mako guda Biden ya tara fiye da adadin da ake bukata na kuri’u 270 a cikin kuri’un wakilan kwaleji 538 don lashe zaben shugaban kasa da za a kaddamar ranar 20 ga watan Janairu.
A cikin wani bayani, Trump ya fadi game da Biden cewa, "Ya yi nasara ne saboda an yi magudi a zaben."
Shugaban ma’aikatan fadar White House mai jiran gado a gwamnatin Biden, Ron Klain ya fada wa shirin Meet the Press na NBC cewa sakon Twitter da Trump ya fitar ba shi ne zai maida Biden shugaban kasa ba, kuma ba shi ne zai hana masa zama Shugaban kasa ba. Amurkawa ne kadai za su tabbatar da haka.
Jami’an zabe a fadin kasar sun fada wa Muryar Amurka da wasu kafafen yada labarai cewa basu gano wata shaidar tafka magudin zabe ba sai dai wasu ‘yan kananan matsaloli na kidaya kuru’u a ranar zabe wadanda ba za su iya sauya nasarar da Biden ya yi ba, kana ba za su iya bai wa Trump damar yin tazarce na wani wa’adin shekaru hudu a fadar White House bA.