‘Yan Najeriya da dama sun fara rungumar tsarin sufurin jiragen kasa yayin da kudin shigar bangaren ya karu zuwa Naira biliyan 1 da miliyan 690 a zango na 2 na shekarar 2024 da muke ciki, abinda ya nuna samun karuwar kaso 53. 14 cikin 100 idan aka kwatanta da naira biliyan 1 da miliyan 100 da aka samu a irin wannan lokaci a bara.
A bara, hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta tara naira biliyan 1 da miliyan 70 a matsayin kudin shigar da ta samu daga fasinjoji.
A cewar rahoton, jumlar fasinjoji dubu 689 da 263 ne suka yi balaguro ta jirgin kasa a zangon na 2 na shekarar, inda aka samu karuwar kaso 45. 38 cikin 100 idan aka kwatanta da fasinjoji dubu 474 da 117 da aka samu a irin wannan zango a 2023.
Haka kuma adadin kayan da aka yi safararsu ta jirgin kasa sun karu matuka, inda aka yi jigilar tan dubu 143 da 759 a zango na shekarar da muke ciki, abinda ya haura daga tan dubu 56 da 936 da aka gani a irin wannan zango a 2023.