A shirin Harshe Da Karin Magana har yanzu muna tare da babban malami Dakta Abdullahi Garba Imam, na kwalejin Mallam Aminu Kano.
Cikin wannan makon zamuyi duba ne akan Karin Magana mai korewa, wanda shine ake amfani da kalmomi na korewa wadanda suka hada da ban, ba, baya, bata da sauransu. Missalin irin wannan karin magana kuwa shine “ban san ana yi ba wai kunu a makwabta” wato dai tunda kunu ba kanshi yake yi ba balle aji.
Haka kuma ana cewa “ban san ana harara taba sai ido ya fado” to wannan korewa ne domin yana nuna indai har ido bai fado ba to bai san ana hararar ba wato ya zamanto a banza ake kenan. “ban damu ba wai anyiwa barawo sata” anan dai barawo na nuna bai damu ba saboda shima yana yin satar ne.
Saurari cikakkiyar tattaunawar cikin sauti…