Yanzu dai za a sake rufe canjin a ranar gona ga watan Faburairun nan.
Kazalika karin ya sa wadanda ke dari-darin karbar tsoffin kudin sun daina inda su ka cigaba da karbar tsoffin kudin.
Nan titunan Abuja ne inda mutane kan zagaya daga wannan na’urar canjin zuwa waccar don neman sabbin kudi amma sai su samu wayam.
Tun gabanin ma kara wa’adin daga sanarwar gwamnan babban bankin Godwin Emefile, mutane kan wuni a bankuna don shigar da tsoffin kudin su asusu amma ba sa samun sabbin kudin.
Har yanzu shugabannin al’umma ba su hango kara wa'adin ne maslaha ba inda su ke cewa barin kofa a bude na yin canjin har tsoffin kudin su kare shi ya fi zama a'ala.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ba alamar sassauci ga jama’a a tsarin.
Komred Muhammad Aliyu Wayas shugaban kungiyar kare ‘yancin dan-adam ne a arewa maso gabar da ke cewa ba laifi a kara wa’adin in an bi tsarin da ya dace.
A nasa ra’ayin Malam Hamza Adamu barin kofa a bude na canjin har tsoffin kudin su kare shi zai taimaki jama’a.
Har yanzu dai ba wadatar tsoffi balle sabbin kudin a hannun mutane da hakan ya sanya musamman talakawa zama cikin zullumi da kin jinin gwamnatin Buhari wacce ta shigo ana ayyururui da kuma alamun za ta gama ana wayyo Allah.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5