Sashen dalibai na gamayyar kungiyoyin arewacin kasar ya koka game da karin kudin makaranta musamman na jami’oi a sassa daban-daban na yankin lamarin da a cewar sashin zai kara kaifin matsalolin.
A wata hira ta musamman da shugaban sashen dalibai na gamayyar kungiyoyin arewacin kasar kwamared Jamilu Aliyu Charanchi ya bayyana matukar damuwarsu game da wannan kari na kudin makarantu lamarin da a cewarsa zai haifar da karin masu zaman kashe wando da aikata miyagun laifuka.
Hasashe ya yi nuni da cewa idan aka dore da wannan karin kudin makarantu da daliban ke kuka akai, akwai yiyuwar mata su fi yawa wajen fita daga makaranta kasancewa a lokutan baya ba’a cika ba karatun ya mace wani fifiko ba balle yanzu da ake fama tsadar rayuwa, kamar yadda Dakta Muhammad Nawaila malamin kwalejin ilimi a Najeiriya ya bayyana.
Duk kokarin jin ta bangaren gwamnatin kasar game da dalilan kara kudin makaranta da dalibai ke biya abin ya ci tura.
Shugaban gamayyar kungiyoyin arewacin kasar Nastura Ashir Sheriff ya baiwa gwamnatin Najeriya shawarar ta hakura da karin kudin makarantu, inda ya bukaci ta rage kudaden da ake kashewa a bubuwan da ba su da wani muhimmaci a kasar don zuba su a bangaren sha’anin ilimi.
A karshe dai sashen daliban ya bukaci dukkan daliban makarantun jami’o’i da ke arewacin kasar da su kasance masu bin doka da oda wajen bayyana damuwarsu ga wannan lamari.
Bincike ya yi nuni da cewa Najeriya ce kasa ta 14 cikin kasashen duniya da ke da mafi yawan al’umma matasa.