Karin Bayani Akan 'Yan Matan Chibok

Wasu 'yan matan Chibok da aka sako

Yawancin iyayen ‘yan matan da aka sako ta kafar radiyo suka ji labarin kamar yadda shugabn kungiyar iyayen ‘yan matan Yakubu Inkeki ya shaidawa Muryar Amurka a wata fira da aka yi dashi. Amma shi karan kansa ya kalla ya kuma ji a kafar talibijan.

Bayan Yakubu Inkeki ya ji labarin ya kira minista mai kula da ma’aikatar harkokin mata wadda kuma ta tabbatar masa da labarin har ma ta bashi sunayen wadanda aka sako.

Yace ya kwatanta sunayen da aka bashi aka kuma aika masa ta wayar tarho da rajistar da yake da ita. Ya ga akwai sunayensu cikinta kana ya san abun da ya ji ya kuma karba a rubuce gaskiya ne.

Yace kodayake babu diyarsa cikin yaran, amma yayi murna tare da yiwa Allah godiya da soma amsa addu’o’insu. Sako yaran ya bashi tabbacin cewa nasu ma idan suna da rai za’a sakosu .

Shugaban Najeriya a yayinda aka gabatar masa da 'yan matan

Baicin zantawa da Yakubu Inkeki, Muryar Amurka ta tattauna da wani Mr. Amos wanda yarsa Comfort na cikin 21 da aka sako. Yace shi da yarsa sunyi kukan murna kafin su natsu su yi tadi.

Mr. Amos yace ya tambayi diyarsa ta fada mashi irin rayuwar da suka yi. Tace da farko da aka kamasu ‘yan Boko Haram sun kula dasu da abinci da sauran abubuwan rayuwa amma da tafiya tayi nisa suka soma rasa abinci su ma sai abun ya shafesu.

Comfort ta shaidawa mahaifinta cewa an rabasu rukuni rukuni ne. A nata rukunin su 114 ne. Tace ranar da za’a sakesu sai aka ce suyi layi kana daga kan yarinya ta farko aka kirga ‘yan mata 21 aka ce su tafi an sakesu. ‘Yan Boko Haram din suka yi ma sauran fatan cewa su ma nan ba da dadewa ba za’a sakesu.

Dangane da cewa ko an tilasta masu suyi aure ko kuma ayi lalata dasu sai Comfort tace babu wani abu makamantan wannan. Tace ba’a yiwa yarinya aure sai da yaddarta. Kungiyar ta ba yaddar yarinya mahimmanci kwarai. Tace yakamata a gode masu tare da gwamnatin tarayya wadda ta matsa sakosu.

Akan ko wasunsu sun rasa rayukansu sanadiyar hare-haren jiragen saman Najeriya, Comfort ta karyata batun. Tace dukansu suna nan da rai.

Bisa ga bayanin da Comfort tayi duka su 197 suna nan da rai. Yanzu da aka sako 21 ‘yan matan da suka rage sun kai 176. Wadannan ne gwamnatin tarayya zata cigab da matsa sakosu.

Mr. Amos ya bayyanawa Muryar Amurka cewa bisa ga abun da aka fada masu gwamnati ta dauki nauyin kula da ‘yan matan tare da basu abinci da magunguna da iliminsu. Yace gwamnatin tarayya tayi masu alkawarin gina masu makarantu kuma su iyaye sun amince da hakan.

Ga firar da Grace Alheri Abdu tayi.

Your browser doesn’t support HTML5

Karin Bayani Kan 'Yan Matan Chibok - 7' 12"