Karfin Kudin Naira Ya Fadi Fiye Da Na Shekaru Da Dama 

Faduwar Darajar Naira

Karfin kudin Najeriya ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da dalar Amurka a kasuwannin gwamnati, kuma daga dukkan alamu lamarin na iya kara ta'azzara a 'yan kwanaki masu zuwa.

WASHINGTON, D.C. - Bayanan da aka samu daga asusun FMDQ, dandalin da ake amfani da shi wajen bin diddigin yadda kudaden gida ke gudanar da ayyukansu a cikin harkar kasuwanci na hukuma, sun nuna cewa, a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, 2023, darajar Naira ya na N463.50 akan kowace dala.

Naira

A karshen cinikin ranar Litinin, 3 ga watan Afrilu, an yi musayar hannayen jari dala miliyan 175.40, wanda ke nuna raguwar kashi 6.9% ko dala miliyan 12.97 idan aka kwatanta da zaman da ya gabata, in ji Businessday.

Karin hakan an samu karuwar kudaden kasashen waje daga ’yan Najeriya masu tafiya, masu shigo da kaya, da masu zuba jari da ke neman dawo da abin da suka samu.

A halin da ake ciki kuma, bisa bin umarnin CBN, bankunan Najeriya goma sun bayyana sunayen kwastomomin da ke sEyan dalA da rahusa amma su koma su sake siyarwa su samu riba a kasuwa.

Babban banbanci da ke tsakanin kasuwar bayan fage da kuma farashin a hukumance ya kara bunkasa sabili da wasu marasa kishin kasa da ke neman cin kazamar riba.