Suna nazari ne akan yadda za'a yi zaben ba tare da musgunawa jama'a, ko dage zaben ko kuma sauya alkaluma ba.
Shin hukumar zaben nada duk kudaden da take bukata da kayan aiki kuwa? Tana da isassun ma'aikatan da zasu gudanar da zaben? Kawo yanzu wasu basu samu katin zabe na dindindin ba. Babu wani kokari na canzawa kwamishanonin zabe wurin aiki ko kuma wani takamaiman bayani. Ba'a san yawan wadanda suka samu rajista ba.
Mataimakin daraktan dake kula da hulda da jama'a na hukumar zaben Nic Dazan ya fadi yawan wadanda aka yiwa rajista a zaben da ya gabata na 2011. A shekarar yace sun yiwa mutane miliyan saba'in da biyu rajista wadanda shekarunsu na haihuwa suka kama daga 18. An basu katuna na wucin gadi kafin a yi masu na dindindin.
Akan tsayawa a runfunan zabe domin a ji sakamakon zaben, wato hanyar nan ta kasawa da tsarewa, masu jefa kuri'a sun bayyana ra'ayoyinsu. Alhaji Muhammadu Jami'u na cikin masu kada kuri'a. Yace hukumar zabe ko INEC ta tabbatar cewa a sanarda sakamakon zabe a kowace rumfa aka yi zaben. Kada ma a ce za'a je wani wuri domin za'a jawo rikici ke nan. A yi zaben da kowa zai iya yadda dashi.
Abba Sa'idu Lau wani malamin firamare yana ganin abu mafi mahimmanci shi ne gudanar da zaben lami lafiya.
Labarai sun nuna cewa hukumar zabe bata hana a kasa a tsare ba matukar yin hakan ba zai kawo fitina ba. Masanin harkokin siyasa Dr Sadiq Abba ya duba mahimmancin sanarda sakamakon zaben a rumfunan zaben. Yace magudin zabe na faruwa ne idan an kai kuri'u matattara. Tsakanin wannan rumfa zuwa waccan runfar ake tafka magudi.
Shugaban hukumar zaben ta INEC Farfasa Attahiru Jega ya fadi hanyar da yake gani ana bi ana tafka magudi.Yace mafi yawan mutane zasu fito ne tunda sassafe kafin karfe goma an soma raguwa. Tsakanin karfe daya zuwa biyu kusan kowace mazaba daga jami'in zaben sai ko dansanda domin babu mutane.'Yan siyasa sun gane sai suna anfani da wannan lokacin su saye duk sauran kuri'a a yi dangwale.
Saidai hukumar tace ta dauki duk matakan da zasu hana a yi magudi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5