Hukumar Zaben Nijeriya (INEC), ta ce ta kammala aikin ba da katin zabe a jihar Naija. Hukumar ta ce aikin ya yi kyau saboda sama da kashi 70 cikin dari mutanen jihar Naija sun sami katin nasu .
Wakilinmu a Minna Mustapha Nasiru Batsari ya ruwaito kakakin hukumar INEC a jihar Naija, Madaki Muhammad Wase na cewa duk da yake sama da kashi 70 cikin dari na mutanen sun kada kuri’arsu, wannan bay a nufin an kammala saboda za a cigaba da bayar da katin a ofisoshinsu da ke kananan hukumomi daga yanzu har zuwa lokacin zaben.
To amma fa wasu mutane- musamman ma ‘yan jam’iyyar adawa na bayyana damuwa game da yadda hukumar ta INCE ta gudanar da aikin bayar da katin. Jami’in Yada Labarai na jam’iyyar APC a jihar Naija, Mr Jonathan Batsa y ace akwai matsaloli da yawa. Y ace har inda aka ce za a rinka yin rajista din ma ba a yi saboda INEC ba ta kai na’urorin aikin ba. Y ace adadin kashi 70% da INEC ke ikirarin sun sami katin ma ban a gaskiya ba ne saboda saboda akwai shakku game da yadda su ka yi wannan kididdigar. To amma a bangaren jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, Mataimakin shugaban jam’iyyar Barr. Tanko Beji, wanda wakilinmu ya tuntuba don jin ra’ayinsu, y ace shi ba zai ce komai ba saboda ya yi mako guda baya jihar saboda ya yi wata tafiya. To amma sabon Kwamishinan hukumar INEC a jihar Nasiru Ayilara y ace zai yi duk abin da yak e iyawa wajen ganin an yi zabe na gaskiya.