Kansiloli a Jihar Neja Sun Gamu da Wulakanci

Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja.

Wasu tsofaffin Kansilolin da yawan su ya kai dari hudu, a jihar Neja, dake tarayyar Najeriya, sun koka saboda cin mutuncin da suka ce anyi masu a gidan Gwamnatin jihar Neja, dake Minna.

Wasu tsofaffin Kansilolin da yawan su ya kai dari hudu, a jihar Neja, dake tarayyar Najeriya, sun koka saboda cin mutuncin da suka ce anyi masu a gidan Gwamnatin jihar Neja, dake Minna.

Tsofaffin Kansilolin, dai suka ce sun je gida Gwamnatin jihar, ne a bisa gayyatar da aka yi masu da nufin warware matsallar bashin da suka ce suna bin Gwamnatin jihar, amma sai suka tarada wulakanci kamar yada wasu daga cikin su suka fadi cewa an maida su tabkar gugar yasa.

Babban sakataren gidan Gwamnatin jihar Neja, Alhaji Hamisu Jankaro, wanda shine ya karbe tsofaffin kansilolin, yace a iya sanin su babu wani wulakancin da aka yi masu, sun dai baiyana koken su kuma aka ce za’a isar da sakon nasu ga Gwamna jihar, daga bisani kuma aka basu Naira Milyan daya su raba, a tsakanin su.