Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Raba Katunan Zabe Fiye da Miliyan 41


INEC
INEC

Biyo bayan cecekucen da ake yi akan raba katunan zabe INEC ta musanta zargin cewa aikin yana tafiyar hawainiya wanda ka iya kawo cikas.

Bugu da kari hukumar zaben zata raba na shekarar 2011 da ta tantance da wadanda da basu yi rajista ba da kuma wadanda babu sunayensu sabili da lalacewar naurorinta duk an yi masu katuna.

Kafin a gudanar da zabe kowa zai amshi katinsa. Wai an riga an kai duk katunan a kananan hukumomi sabili da haka kowa yaje ya amshi nashi. Babu wata hujja yanzu. Kada mutane su zauna su ce INEC ce bata fitar da katunan ba. Yanzu kam tayi. Duk wanda aka yiwa rajista yaje ya amshi katinsa.

Akan karatun sakandare da aka ce Janaral Buhari bai gama ba INEC tace ita bata da hurumin hana wani dan takara tsayawa zabe muddin jam'iyyarsa ta mika sunansa ga hukumar. Idan wani bai gamsu ba sai ya garzaya kotu domin a biya masa bukatarsa. Amma hukumar ta gamsu da dan takarar.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG