Sai dai manoman kasar na ci gaba da kokawa kan koma bayan da noma ke samu saboda barazanar tsaro.
Tun kimanin shekaru biyar da suka shude, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti na musamman akan wannan manufa ta raya fannonin samun kudade marasa nasaba da albarkatun mai, da nufin rage dogaro da kasar keyi akan kudaden cinikayyyar man.
Shugaban kwamitin kuma gwamnan Jigawa Badaru Abubakar aikin kwamitin nasu ya fara haifar da sakamako mai alfanu.
A cewar gwamna Badaru tuni tasirin wannan tsari ya bulla yankunan karkarar Najeriya.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da manoma Najeriyar ke korafi akan jinkirin samun tallafin gwamnati a kasar.
Kamar yadda Arc Kabiru Ibrahim shugaban kungiyar Manoman Najeriya, ya yi karin haske a kai.
Yace baya ga haka, tsaro shine babbar matsalar da ke dakile cigaban manoma da kuma dakushe burin su na wadata kasa da abinci.
Saurare cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5