Kimanin shekaru biyar kenan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin bayar da bashi ga manoman shinkafa a jihar Kebbi inda aka baiwa dubban daruruwan manoma bashin kayan noma.
Duk da kalubale da manoma da shi kansa shirin ya fuskanta manoma sun bayar da shinkafar da aka yi dala wadda ta kunshi sama da tan 200,000.
Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ne ya bayyana yadda za'a yi da shinkafar inda ya ce kamfanonin sarrafa shinkafa 24 da za'a baiwa ita kuma a ba su bashin sayenta ta yadda wadanda suka noma ta za su iya biyan bashin da suka karba.
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya ce wannan ba karamar nasara ba ce aka samu cikin shekaru biyar kacal da soma wannan tsarin.
Wannan nasarar ta bayar da dama ga Jamhuriyar Benin nuna ra'ayin jin kawance da Najeriya akan noman shinkafa.
Isa Salisu Sanata ne, kuma yana cikin ayarin da shugaban kasar ta Benin ya turu Najeriya akan wannan batun.
Ko wane amfani Najeriya za ta samu ga kawancen, tambayar da aka yi wa Aminu Muhammad Goronyo shugaban kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya, inda ya ce gwamnati da jihar Kebbi za su samu amfani gaba daya.
Magabata irin mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na ganin cewa idan kowa ya gudanar da nauyin da ya rataya kansa ta wannan haujin na noman to za'a ci gaba da samun nasarori masu yawa da amfani.
A saurari rahoton cikin sauti daga Muhammad Nasir: