Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da al’umar jihar ta Kano ke dakon hukuncin kotun kolin Najeriya dangane da shari’ar kujerar gwamnan jihar.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta shawarci mazauna birnin da kewayen Kano suyi watsi da kokarin da wasu rukunin mutane keyi na samar da yanayin fito-na fito, musamman a tsakanin jami’an tsaro da jama’ar gari.
Sanarwar tace kwamishinan ‘yan sanda Mohammed Usaini Gumel ya bada umarnin zakulo wadanda suka cinna wuta a sakatariyar karamar hukumar Gwale a daren shekaranjiya, wacce ta kona ofisoshi da dama tare da barnata takardun gwamnati masu yawa.
Al’amarin dai ya faru ne sa’oi kalilan bayan da babbar kotun Kano ta bada umarnin mayar da shugaban karamar hukumar Khalid Ishak wanda Majalisar dokokin jihar ta Kano ta dakatar dashi watanni uku da suka gabata, saboda zargin ya aikata ba dai-dai ba.
To amma, Alhaji Khalid Ishak wanda ya bayyana mamaki kan yadda gobarar ta tashi ya yi zargin cewa, da gangan wasu suka cinnata domin firgita shi. Ya kuma kara da cewa, ”abu ne wadda lallai dole mu bincika kuma zamu rubuta rahoton gaggawa ga jami’an tsaro, kodayake dama tun fari mun sanar da su cikin sauri bayan da gobarar ta tashi”.
Al’amarin dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da batun shari’ar gwamnan Kano ke kara dumama yanayin siyasar jihar yayin dake ake dakon hukuncin kotun kolin Najeriya dangane da batun.
Sai dai Sanata Mas’udu Eljiril Doguwa, guda cikin dattawan Kano yace baya ga rashin hadin kai da son zuciya a tsakanin ‘yan siyasar Kano, wanzuwar kafofin sadarwa na social media a wannan zamani na cikin abubuwan dake zafafa wannan batu dake nema ya zama barazanar tsaro ga al’uma.
“Tasirin wannan social media da kake gani, a da can sai idan munji Radio Najeriya Kaduna ta fada ko kuma Radio Kano, amma yanzu tun kafin alkali ya zauna a kujerar sa, wani ya dauki wayar sa ya rubuta labarin karya akan hukuncin kotu, ya jefa mutane cikin rudani”.
Yanzu kallo ya koma kan kotun kolin Najeriya wadda ake sa ran zata yanke hukuncin karshe game da wannan kujera ta gwamnan Kano.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5