Kamfanonin Rarraba Hasken Lantarki Sun Kara Farashin Mita  

Sabon farashin mitocin zai fara aiki ne a ranar Talata, 5 ga watan Nuwambar da muke ciki, a cewar sakonnin da kamfanonin rarraba hasken lantarkin suka wallafa a shafukansu na sada zumunta.

Kamfanonin rarraba hasken lantarki a Najeriya (DISCOS) sun kara farashin mita.

Sabon farashin mitocin zai fara aiki ne a ranar Talata, 5 ga watan Nuwambar da muke ciki, a cewar sakonnin da kamfanonin rarraba hasken lantarkin suka wallafa a shafukansu na sada zumunta.

Da wannan sabon karin, farashin mita mai layi daya ya karu zuwa N149, 800 daga N117, 000. hakan ta danganta ne kamfanin rarraba lantarkin da kuma dan kwangilar daya samar da mitar.

Bincike ya nuna cewa kamfanin rarraba hasken lantarki na Eko ya tsayar da farashin mitarsa mai layi daya a tsakanin N135, 987.50 da N161, 035 sannan mai layi 3 a tsakanin N226, 600 da 266, 600.

A nata bangaren, kamfanin rarraba lantarki na Ibadan ya bukaci abokan huldarsa su biya tsakanin N130, 998 da N142, 548 akan mita mai layi daya sannan su biya tsakanin N226, 556.25 da 232, 008 ga mita mai layi 3.