Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Layin Wutar Lantarkin Najeriya Ya Rushe A Karo Na 2 Cikin Kwanaki 3


Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya
Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya

Binciken da aka gudanar akan shafin dake bada bayanai akan babban layin lantarkin na Najeriya (niggrid.org), ya nuna cewa da misalin karfe 11.30 na safiya yawan lantarkin dake kan babban layin ya sauka gaba daya al’amarin da ya shafi ilahirin kamfanonin dake samar da lantarkin a fadin kasar.

Babban layin wutar lantarkin Najeriya ya ruguje a karo na 2 cikin kwanaki 3, abin da ya jefa sassan kasar da dama cikin duhu.

Binciken da aka gudanar a kan shafin dake bada bayanai a kan babban layin lantarkin na Najeriya (niggrid.org), ya nuna cewa da misalin karfe 11.30 na safiya yawan lantarkin dake kan babban layin ya sauka gabadaya zuwa matakin babu ko megawatts daya, al’amarin da ya shafi ilahirin kamfanonin dake samar da lantarkin a fadin kasar.

Haka suma wasu daga cikin kamfanonin rarraba hasken lantarkin sun tabbatar da hakan a shafukansu na sada zumunta.

“Muna sanar daku cewa mun samu katsewar lantarki a yau 7 ga watan Nuwambar 2024 da misalin karfe 11.29 na safiya, al’amarin da ya shafi samar da wutar a kan layukanmu,” kamar yadda kamfanin rarraba hasken lantarki na Ikeja (EKDC) dake kula da wasu sassan Legas ya wallafa a shafinsa na X.

Shima kamfanin rarraba hasken lantarki na Eko (EKEDP) ya shaidawa abokan huldarsa game da “game da yiyuwar katsewar wutar”

“Muna masu sanar daku cewa da misalin karfe 11.29 na safiya, a yau 7 ga watan Nuwambar 2024, mun samu katsewar lantarki a gabadayan layukanmu,” a cewar EKEDP.

Haka kuma, kamfanin rarraba hasken lantarki na Jos ya wallafa cewa, “katsewar lantarkin da aka samu a jihohin dake karkashin kulawarmu ta faru ne sakamakon rushewar babban layin lantarki na kasa.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG