Kamfanin NNPC Ya Bayyana Musabbabin Karancin Mai a Abuja

Hedikwatar NNPC.

Saboda haka kamfanin NNPC ya shawarci 'yan Najeriya da su daina ribibin sayen man irin na fargaba, don kuwa akwai isashen man.

Kamfanin Mai Na Najeriya, NNPC, ya ce ya lura da sake bullar dogayen
layuka a gidajen mai a wasu sassan babban birnin kasar Abuja, wanda
hakan ya biyo bayan karancin yadda ake lodin mai a defo defo da
kuma hakan ke faruwa, galibi, a lokutan dogon hutu, irin dai wanda akai na
karamar Sallah a kwanan nan.

Wani karin dalilin kuma na ganin dogayen layin man shi ne yadda yadda
aka sami karin sayen man da ya zo daidai da yadda akasarin mazauna
birnin ke dawowa daga dogon hutun da su ka je.

Wata sanarwar da babban manajan sadarwa na kamfanin mai na kasa NNPC, Garbaddeen Muhammed, ya sanyawa hanu, ta ce kamfanin man da takwaransa hukumar da ke tsara albarkatun mai na kasa, NMDPRA, da ma yan kasuwar man da sauran masu ruwa da tsaki na daukar matakai don shawo kan matsalar.

Ku Duba Wannan Ma Yadda Shirin Operation Dakatar Da Barawo Ke Tasiri A Neja Delta

NNPC na tabbatar wa mazauna babban birnin tarayyar kasar da ma kuma
sauran yan Najeriya cewa akwai fa mai shake a ma'ajiya da ya kai lita
Bilyan daya da Milyan Dari biyar da zai wadaci Najeriya na fiye da
kwanaki arba'in da biyar

Saboda haka kamfanin NNPC ya shawarci 'yan Najeriya da su daina ribibin sayen man irin na fargaba, don kuwa akwai isashen man.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:

Your browser doesn’t support HTML5

NNPC Ya Yi Bayanin Karancin Mai