Kamfanin Motor Ford CO. Na Shirin Kera Gado A Cikin Motoci Masu Tuka Kansu.

Kamfanin dake kera motoci ta Ford Co. zata kera gado a cikin mota wadda na gwaji wa yankin Maimi-Dade

Kamfanin dake kera motor Ford Co. zai kera gado a cikin mota wadda za a yi gwajin ta a yankin Maimi-Dade.

Mai kerar motocin da abokan aikin sa, gidan abincin Domino’s Pizza, wani kamfanin tasi da ake kira ride- hailing Lyft da wata kamfanin sakkoni na delivery Postmates – za su fara wani shiri don ganin yadda mutane za su amsawa wasu sabbin kirar motoci da aka kera masu aiki da kansu.

Motar zata tashi kanta kuma kamfanin Ford Argo, ya riga ya tura motocin yankuna da takardar nuna hanya da za’a yi amfani da ita yayin tuki, Kamfanin Ford zai kuma kera sabon wurin ajiye motacin masu tuka kansu na farko a birnin Miami, inda motar zata koyi yadda zata dauki mutane da ajiye su.

Za’a kara bayyana wasu ayyuka na motocin wadanda suka hada da wani sabon yanayi a wayar sadarwa da aka sakawa suna Chariot wanda zai bari motocin su yi aiki da kansu. Duk a kokarin kamfanin Ford na neman kasuwanci na sababbin motocin masu aiki da kansu kuma su fara aiki a kan hanya a shekarar 2021.

Wannan shine cigaban kamfanin motoci, idan yawancin mutanen duniya zasu zauna a manyan birane, muna bukatar fahimtar yadda zamu yi jigalar mutane, a cewar John Kwant, mataimakin shugaba a kamfanin Ford na city solutions, wanda ya kulla yarjejiniyar da Miami-Dale.

Muna son mu kasance mune kan gaba saboda muna son mu ba al’ummar mu ra’ayi dabam,’’a cewar Carlos Gimenez, shugaban yankin Miami-Dade, tunda ga nan gida da kuma manyan birane 34 da mutane miliyan 2.7.