Jami’an ‘yan sanda sun kama wani matashi mai shekaru 15 da haihuwa mai suna Idris, wanda ke matakin farko na zangon karatun makarantar sakandire, bisa zargin sa da hannu a wata kungiyar asiri a jihar Legas.
Kamar yadda mujallar Daily Post ta wallafa, an kama Idris, wanda shi dalibi ne a wata makarantar kudi, kuma ajin sa guda, tare da wasu da ake zargi duk ‘yan kungiyar asiri ne su 56 a jiya litini, kuma yanzu haka suna shalkwatar ‘yan sanda dake Ikeja, a jihar Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa an cafke matasanne a cikin karshen makon da ya gabata tare da taimakon jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga a cikin daji yayin da suke kokarin shigar da sababbin ‘yan kungiyar ciki harda Idris.
Jami’an sun bayyana cewa an sami matasan da bindigogi guda biyu kirar gida da albarusai da dama tare da su a lokacin da aka yi ram da su.
Idris ya bayyanawa mujallar Punch, cewar wani mutum dan unguwar su ne ya sai masa lemu ya sha, bayan nan ya bukaci ya raka shi wani guri, daga nan ne suka rufa masa fuska sa’an nan suka kai shi wani wuri inda suka tsaga babban yatsan sa suka debi jini, ya kara da cewa “yayin da muke kokrin tafiya misalin karfe hudu ne na ji harbin bindiga sai kawai ‘yan sanda suka kama mu”.
Wani daga cikin matasan da aka kama su tare mai suna Adebayo, mai shekaru 25, da haihuwa ya bayyana cewa suna hanya ne tare da ‘yan uwansa zuwa wani biki, sai wasu suka tare su suka kwace masu wayoyi da katunan su na ATM, sa’annan suka rufe masu fuskoki kafin suka kawo su wurin, ya kara da cewa su ma an tsaga masu yatsu kuma an debar masu jini.
Kwamishinan ‘yan sanda Edgal Imohimi ya bayyana bakin cikinsa musamman ganin yadda ake samun karuwar matasa cikin kungiyoyin asiri.
Facebook Forum