Babban abunda ya sa na fara sana'ar waka bai wuce cika burina, na isar da sakonnin da suka shafi zamantakewar yau da kullum, da kuma fadakarwa mussaman ma ga matasa, a tabakin Ahmad Idris wanda aka fi sani da Ahmad Delta.
Ya kara da cewa shi mawakin nanaye ne, wato blues kuma ya fara harkar waka ne sakamakon sha’awa da birge shi da wasu mawakan Hausa keyi, kamar su Muddasir Kasim, da Sadi Sidi Sharifai, da suke yi, hakan yasa ya fara waka.
Delta, ya kara da cewa bayan sha’awar waka da ya keda, daga bisani sai ya fara rubuta waka har ta kai shi ga ya fara rerawa, Ahmad Delta ya ce a mafi yawan lokuta wakokinsa na zaburar da matasa tare da tunzura su, don sanin muhimmanci rike sana’a da neman halaliyarsu, ba tare da sun dogara da wani yayi musu wata alfarma ba.
Delta ya ce kafin waka yana sana’arsa ta hannu na dinkin tela, amma hakan bai hana masa tsunduma cikin sana'ar waka ba. Ya kara da cewa babban burinsa bai wuce wakokinsa suyi tasiri a zukatan alumma ya kuma yi fice ba.
Facebook Forum