Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Binciken Hukumar Lafiya Ta Duniya Kan Adadin Shan Taba Sigari A Fadin Duniya


A shafin ta na yanar gizo, hukumar lafiya ta duniya WHO ta wallafa cewa a shekarar 2015, sama da mutane miliyan goma sha daya ne ke zukar taba sigari, hukumar ta kuma bayyana cewa yayin da shan taba sigari ke raguwa a wasu sassa na duniya, lamarin kara muni yake a kasashen dake yankin gabashin maditaraniya da nahiyar Afirka.

Hukumar ta zaiyana wasu muhimman batutuwa a game da shan taba sigari a shafin ta kamar haka:

.Taba sigari na hallaka kusan rabin masu shan ta.

.Taba sigari na hallaka sama da mutane miliyan 7, a kowace shekara, sama da miliyan 6 na wadanda suke mutuwa taba ce ke hallaka su kai tsaye, kusan mutane dubu 890,000 kuma na mutuwa ne a sakamakon shakar hayakin tabar da suke yi.

.Kusan kasha 80 cikin dari na mashaya taba sigari a zama ne a kasashe masu fama da talauci da kuma kasashe masu matsakaicin tattalin arziki.

A shekarar 2016, babban bankin duniya ya fitar da wani daftari na yawan shan taba sigari a duniya inda ya bayyana cewa daga shekarar 2000 zuwa 2015, shan taba sigari ya karu a kasashe 27, rahoton ya bayyana cewa akasari kasashe ne dake fama da matsalolin tattalin arzki.

Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya karu da kusan kashi talatin cikin dari a Indonesia, ya kuma bayyana cewa sama da mutane Miliyan 70, ne ke zukar taba sigari a kasar. Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa idan ba a dauki matakin shawo kan lamarin ba, za a sami karuwar yawan mace mace a sakamakon shan taba sigari.

Rahoton ya bayyana cewa a kowace kasa, yawan adadin maza masu shan taba sigari ya dara mata.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG