Kamfanin nan mai shafin bincike na yanar gizo da ake cewa Google da turanci, ya amince daya gayawa mutane masu amfani da shafin sa yadda yake amfani da bayanansu dayake adanawa a lokacin da suke bincike akan shafin, yin hakan ya biyo bayan wani bincike da hukumar kiyaye bayanan mutane a yanar gizo ta Birtaniya tayi, inda ta gano cewar manufofin kamfanin kan kare sirrin bayanan mutane kadaran kadahan ne.
Ofishin kwamishinan harkokin yada labarai ya fada a wata sanarwar cewa ya bukaci kamfanin Google, da ya sanya hannu a hukunce cewar kan ranar 30 ga watan Yuni zai yiwa lamarin gyara sa’anan kuma ya dauki karin matakan inganta lamarin cikin shekaru biyu masu zuwa.
Binciken da ofishin kwamishinan harkokin yada labaran yayi akan manufofin kare sirin bayanan mutane da kamfanin na Google ya fitar a shekara ta 2012, wanda suka hada da wasu manifofinta wajen saba’in daya ke amfani dasu a matsayin manufa daya, inda take tatattara bayanan mutane a duk inda ake amfani da shafin na Google, wanda ya hada da shafin bidiyo na YouTube na sa hotunan vidiyo, dana aikawa da sakonin Gmail, harma da shafin sadarwar ta na Googleplus.
Wasu kamfanoni a kasashen Spain da Faransa sun ci tarar kamfanin Google dala miliyan daya da dubu dari biyu, duk kuwa akan manufar san a kare sirrin bayanan mutane da yake tarawa.
Kamfanin Google dai ya ribar dala biliyan 55.52bn a shekara ta 2013.
Your browser doesn’t support HTML5