Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mai Takawa Kilomita 33 Zuwa Aiki Da Dawowa Kakarsa Ta Yanke Saka


Akwai wani mutum anan Amirka, mai suna James Robertson, wanda yake zaune a birnin Detroit dake jihar Michigan. A kullu yaumin James yana yin tafiyar kimanin kilo mita 33. Yana takawa da kafarsa yaje aiki, ya kuma taka ya koma gida a rana, kuma yana yin hakane a lokacin zafi da lokacin sanyi.

An dai wallafa labarin wannan mutumin ne a wata mujallar birnin Detroit, wanda yin hakan ya jawo hankalin wani dalibin jami’ar Wayne mai suna Evan Leedy. Dalibin dai ya bude gidauniya tara gudumawar kudi domin ya sayawa James Robertson mota.

Leedy dai ya bude gidauniya da sunan Robertson, a ranar daya ga watan nan na Fabarairu, burinsa shine ya tara dala dubu biyar,.

To amma abun mamaki a cikin rana guda ya tara sama da dala dubu tamanin da biyar daga sama da mutane dubu biyu.

Za’ayi amfani da kudin domin sayawa Robertson motar, da kuma taimaka mishi wajen wasu abubuwansa na rayuwa.

Haka kuma Leedy yana daukar wasu matakai na ganin cewar Robertson ya samu wadannan kudade da aka tara masa, ba tare da kuma wani ya takura masa daya raba kudin da shi.

Shi dai Robertson yayi kimamin shekaru goma yana aiki a wannan wuri, kuma yana takawa da kafarsa domin babu wata motar haya da ke bin hanyar. Yana kuma yi mamakin yadda mutanen da basu taba sanin sa ba, su taimaka masa.

Baya ga taimakon kudin da mutane suka tara masa, wasu kamfanoni sayar da motoci guda, kamfanin sayar da mota samfurin hoda da Chevrolet sunyi tayin baiwa Robertson kyautar mota.

XS
SM
MD
LG