WASHINGTON, DC —
Mutane uku ne suka rasa rayukansu a wani tashin bom da wani dan kunar bakin wake yakai, jin kadan bayan an tashi daga taron yakin neman zabe wanda shugaba Goodluck ya gudanar a Gombe.
An kai harin ne a layin titin Kashare dake cikin garin Gombe, dake kusa da filin da aka gudanar da yakin neman zaben. Inda za’a iya tunawa a jiya ma an kaddamar da harin bom na kunar bakin wake a gurare biyu a garin na Gombe, tunda farko kuwa kafin hatsarin bom din shugaba Goodluck Jonathan, ya bayyana jin dadin sa dangane da irin tarbar da akayi masa a jihar Gombe.
Tuni dai tawagar shugaba Jonathan tabar jihar Gombe, a cigaba da yakin neman zabe data ke kaiwa jihohin Najeriya.