WASHINGTON, DC —
Anyi taron kwamitin musamman na sanya ido kan yarjejeniyar lumana da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyu goma sha hudu suka rattabawa hannu.
Tsohon shugaban mulkin soja janal Abdulsalam Abubakar, ne ke jagorantar wannan kwamiti, janal Abdulsalam Abubakar dai shine ya mikawa farar hula mulkin Najeriya a shekara ta alif dari tara da casa’in da tara (1999), ya dai bada tabbacin cewar kwamitinsa bazaiyi gyangyadi ba kan wannan aiki na kungiyar.
Tuni dai wasu jahohi suka dauki matakan bada hutu a ranakun gangamin ‘yan takara da suke cewa kan matakine na kaucewa tarzoma.