Kamfanin Apple Na Fuskantar Kararraki Akan Ingancin Wayoyinsa

iPhone

Kamfanin Apple yana fuskantar kararraki har kashi biyu kan cewa yana yaudarar masu amfani da wayoyinsa ta hanyar rage ingancin tsoffin wayoyin domin a sayi sabbi.

Babban kamfanin fasahar ya fito ya fadi gaskiyar magana cewa yana rage ingancin wayoyinsa na iPhone 6 da 6s da kuma iPhone 7 ta hanyar aikawa wayoyin wata manhaja da zata gyara wata matsala da take lalata batiran wayoyin.

Wandanda suka shigar da karan suna neman Apple ya dakatar da rage ingancin tsoffin wayoyinsa, kuma ya biya diyya ga mutanen da wannan abu ya shafa wadanda suka shigar da kara a jihar California ranar Alhamis.

Haka kuma jaridar Chicago Sun Times ta fitar da rahotan wani sabon ‘kara da wasu daga jihohin Ohio da Indiana da kuna North Carolina suka shigar, suna neman Apple ya biya su diyya saboda karya dokar kare masu siyayya da yayi.

Bayanan karan da suka shigar na nuna cewa wayoyinsu sun rage karfin aiki daidai lokacin da kamfanin ya fitar da sabbin wayoyinsa.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamfanin Apple Na Fuskantar Kararraki Akan Ingancin Wayoyinsa - 1'04"