Da yake ‘daukar mataki kan korafe-korafen satar fasaha da amfani da aikin wani ba tare da izini ba, Facebook ya sanar da cewa cikin watannin shidan karshen shekarar 2017 ya cire wasu abubuwa da mutane ke kafewa kusan Miliyan uku a dandalinsa.
Wannan mataki da Facebook ya ‘dauka ya biyo bayan wani rahoton fayyace gaskiya na Facebook da aka fitar, kamar yadda wani jami’in kamfanin Chris Sonderby, ya ce “mun yi Imani da fitar da bayanai akan rahotan da muka samu daga masu ruwa da tsaki, wata muhimmiyar hanya ce da zamu yi amfani da ita wajen bayyanawa jama’a yadda muke kare bayanansu.”
Rahotan da aka fitar ya nuna yadda neman bayanai daga gwamnatoci ya karu da kashi 21 cikin 100 a fadin duniya, idan aka kwatantashi da rahotan daya gabata.
Domin kare bayanai a dandalin Facebook ya samar da wata hanya da zata ankarar da mutane idan aka yi amfani da fasaharsu da suka kirkira, missali kamar wakoki do hotunan bidiyo.
Ta haka ne masu fasahar zasu iya aikawa da sakon neman Facebook ya cire abin da aka kafe ba bisa ka’ida ba.
Facebook Forum