'Yan Kamaru yanzu za su iya zaɓar tsakanin Sinopharm na China, Oxford-AstraZeneca da Johnson & Johnson amma jinkirin karban rigakafin daga masu shakkun alluran har yanzu na da yawa.
Kimanin fararen hula 10 ne suka ziyarci asibitin Biyem Assi da ke Yaounde babban birnin Kamaru a yau domin karbar allurar rigakafin COVID-19. Daga cikinsu akwai Olivia Forbi, 'yar shekara 38 mai sayar da kayan lambu.
Forbi ta ce tana son rigakafin Johnson & Johnson tun da ta ji labarin a gidan rediyon kasar Kamaru.
"Na ji cewa Johnson & Johnson na da tasiri fiye da kashi 75 cikin 100 wajen dakatar da yaduwar kwayar ta coronavirus sannan na biyu kuma, zaka dauki allurer sau ɗaya. Sinopharm da AstraZeneca, kuwa allurar sau biyu ne," in ji Forbi.
A ranar 21 ga Yuli, Shugaba Joe Biden ya ba da sanarwar Amurka na jigilar alluran rigakafi miliyan 1.3 zuwa Afirka. Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Gambiya, Lesotho, Nijar, Senegal da Zambia na cikin kasashe bakwai da suka ci moriyar shirin.
Mary Daschbach mai kula da aikin a ofishin jakadancin Amurka da ke Yaounde. Ta ce ta ba da allurar COVID-19 na Johnson & Johnson duda 303,050.