Makarantu da harkar kasuwanci a bangaren kasar Kamaru inda ake anfani da turancin Ingilishi naci gaba da kasancewa kulle.
Hakan ko ya biyo bayan yajin aikin watanni 5 da malamai da lauyoyi suka kaddamar ne, na cewa ana tursasa musu wajen anfani da harshen faransanci.
Wakilin muryar Amurka a birnin Yaounde Moki Edwin Kindzeka, yace shugabannin wannan zanga-zangar su 3 dama wasu mutane 25 daga sashen masu anfani da harshen turanci duk an tsare su kuma an gurfanad dasu gaban kotun sojan kasar a jiya alhamis sai dai kuma an dage sauraren karar.
Wakilin Muryan Amurka yace an jiwo daya daga mutane ukkun da ake tsare dasu wato Bibixy Mancho, na cewa shi kan ba zai taba mantawa da asalin sa ba, yayin da sojoji ke masa rakiya zuwa kotun sojan da suka gurfana.
Sojojin dake musu rakiyar dai sun hana mutane kalilan din da suka fito domin gaisawa da wadannan mutanen, daya daga cikin ire-iren wadanan mutanen ko sun hada da Minang Flora, wadda tace tayo tafiyar kilomita 400 ne domin kawai tazo ta nuna goyon bayan ta ga wadannan mutanen da ake rike dasu.
Tace “nazo ne domin na gansu kuma na kara musu kwarin gwiuwar cewa muna tare dasu, kuma komai dadewa sai mun kai ga biyan bukata wata rana.
Sauran mutanen ko sun hada ne da Nkongho felix Agbor Balla,da Fortem Aforteka dashi Bibixy din ana tuhumar su ne da shirya zanga-zanga a cikin watan December bara, wanda kuma zanga-zangar ta koma fada.
Haka kuma akwai wasu mutane 25 da aka kame baya ga wadannan ukkun, dukansu daga yankin kasar na masu Magana da turancin Ingilishi.
Lauya mai kare wadanda ake tuhuman yace bai dace ace a hadasu wuri guda ayi musu hukunci iri guda ba.