Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Amurka Na Shirin Rage Kasafin Kudi A Ma'aikatar Ilimi


Gagarumin shirin rage adadin kasafin kudi a fannin ma'aikatar ilimi a Amurka, zai yi tasiri matuka gaya ga dalibai da kuma harkokin bincike a harkar ilimi anan Amurka, dama duniya baki daya.

Shugaba Donald Trump, wanda yake fatar ganin ya rage a kalla dala biliyan 9 a kasafin kudin shekarar 2018, wanda yazo dai-dai da kashi 13.5 ga harkar ilimin Amurka. zai bukaci amincewar ‘yan majilisar dokokin Amurka kafin hakan ta tabbata.

Ita ma ma'aikatar harkokin kasashen waje wadda zata fuskacin ragowar kashi 28, an shawarce ta data ci gaba da rike shirin nan da Amurka, ta dade tana taimakawa Amurkawa, dake zuwa kasashen waje karatu dama 'yan wasu kasashen dake zuwa Amurka, karatu a jami'oin Amurka.

Har ila yau da yawan wasu shirye-shiryen musayar dalibai ko kuma wasu fannonin nazari da ake gudanarwa suma zasu fuskanci wannan tsari na raguwar kasafin kudin.

A cikin makonni, zuwa watanni ne za a tafka muhawara game da wannan kasafin kudin na shugaba Donald Trump, wanda abu ne da ake iya canzawa, amma sai dai an riga an fitar da muhimmam bayanan yadda gwamnatin ta kudiri aniyar kashe kudinta a wannan karo.

Hatta cibiyar nazarin samar da zaman Lafiya, daya daga cikin muhimmam wuraren dake da dinbin tasiri game da sasasnta na rikice-rikice na duniya bata tsira ba daga ragewar wannan kasafin kudin

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG