Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Layin Dogo Mafi Girma A Duniya, Ya Zakulo Kayan Tarihin Shekaru 2,017!


Masu aikin hada layin dogo, daga tashar jirgin sama da yafi kowannen yawan hada-hada a duniya, Heathrow zuwa gundumar kasuwancin kasar Ingila, sun tsinci wani tagulla wanda ake tsammanin an bama babban janaral a lokacin mulkin Rumawa a shekarar 245AD, bayan hijirar Annabi Isah.

Abun da ban mamaki ace, wannan Tagullar yayi yawo daga daular Rome, zuwa karkashin kasa a kasar Birtaniya. Haka sun tsunto wata kwalba dauke da kananan kwalabe goma sha biyu. Kana sun tsinci wani kofaton doki, da akayi amfani da shi a zamanin mulkin Rumawa, don sakama dawakai a matsayin safa.

Duk cikin ire-iren abubuwa da suka tsinto a cikin karkashin kasa, a tsakiyar birnin Ingila, sun hada da wasu daruruwan kasusuwan mutane. Kasusuwan na nuna alamun cewar, wasu mutane ne da aka kashe su, biyo bayan saba dokokin gwamnatin wannan lokacin, alamu na nuna cewar an azabtar da su ta hanyar saka su cikin karkashin kasa.

Wani babban abun sha’wa shine, yadda suka gano kwarangwal din wata mata, a rararabe ‘yar kasar Roma, a karkashin kasa dai-dai da babban layin Liverpool dake Ingila. An samu kokon kanta a tsakanin kasusuwan kafafunta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG