Ana gabda kammala daya daga cikin mafi girman gine-gine a fadin kasashen turai. Babban abun mamaki da wannan aikin shine, yadda ake zurfafa gini mai zurfi a cikin karkashin kasa a kasar Birtaniya.
Aikin gadar jirigin kasa da akeyi wanda zai hada babbar tashar jirgin sama, da tafi kowacce hada-hada a fadin duniya Heathrow, da gundumar kasuwanci dake tsakiyar babban birnin Birtaniya. Layin dogon shine layin dogo da yafi kowannen girma a fadin duniya.
Hakan zai taimaka matuka wajen rage yawaitar cunkoso a tsakiyar birnin Ingila, yadda mutane baza su yawaita amfani da motoci ba sai dai jirgin kasa. Babban birnin na Birtaniya nada tsohon tarihi a duniya.
A cewar Mr. Jackie Keily, jagoran aikin, babban abun ban sha’awa da mamaki da wannan aikin shine, yadda suke ratsa tsakiyar birnin Ingila, ta cikin karkashin kasa, batare da wata hatsaniya ba. Kuma aikin ya basu damar kwakulo wasu abubuwa a cikin karkashin kasar.
Daya daga cikin abubuwan da suka tsinto sun hada da wani tagulla, da aka bada shi a zamanin mulkin Rumawa a shekarar 245AD, bayan hijirar Annabi Isah.