Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris, ta kai ziyara jihar Tennessee da ke kudancin Amurka, inda ta caccaki ‘yan Republican da ke majalisar dokokin jihar saboda korar wasu abokanan aikinsu ‘yan Democrat biyu da suka yi daga majalisar.
Sallamar mambobin biyu na zuwa ne bayan wata zanga-zangar neman a kara tsaurara matakan mallakar bindiga da su yi a zauren majalisar.
Yayin wani jawabi da ta yi a jami’ar Fisk da asalinta ta bakaken fata ce, wacce ke birnin Nashville, Harris ta ce an kori ‘yan majalisar dokokin biyu ne saboda sun tsaya tsayin daka don a kare rayukan yara kanana, tana mai nuni da harin da ya halaka wasu dalibai a wata makaranta a Nashville a watan da ya gabata
Mataimakiyar shugaban kasar ta gana cikin sirri da ‘yan majalisar da aka kora, wato Justine Jones da Justine Perason da kuma wata ‘yar majalisar Gloria Johnson ‘yar republican da ta shiga zanga-zanga, wacce ba a kore ta ba, saboda rinjaye da ta samu da kuri'a daya.
Yayin zanga-zangar da suka yi, ‘yan Democrat uku sun doshi gaban zauren majalisar suna rera wakoki, matakin da ya take dokar majalisar na yin komai cikin tsari.