Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Jaddada Aniyarta Ta Taimakon Ghana A Fannonin Tsaro Da Tattalin Arziki 


Ziyarar Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris a Kasar Ghana
Ziyarar Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris a Kasar Ghana

Mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Haris ta gana da shugaban kasar Ghana Nana Akuffo Addo a fadar shugabancin kasar inda suka tattauna akan wasu muhimman batutuwan da suka hada da tsaro da tattalin arziki da dai sauransu.

Taron da suka gudanar a fadar shugabancin kasar Ghana a jubilee house ya samu halartar ministocin gwamnatin Nana Addo da wasu manyan manyan jamian gwamnatin kasar Amurka da ma uwargidar shugaba Nana Addo.

A jawabin da ta gabatar, mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da ke ziyarar kwanaki uku a kasar Ghana tace "Ina nan ne domin tattauna batutuwa da dama da kai, musaman wadda muka yi shekaru biyu da suka gabata a fadar White White House na karfafa alaka da samun anfani bai daya tsakanin kasashenmu ta fannin cigaba tare da tsaron kasar Ghana da ma nahiyar ta Afrika. Amurka ta mai da hankali wajen zuba jari a fannin kiwon lafiya dama cigaban kasar, domin wannan zai anfanar da a'lummar Ghana da nahiyar Afirka tare da Amurka baki daya".

A bayanin nasa, shugaban Ghana Nana Addo ya nuna farin ciki da wannan ziyarar ta mataikiyar shugaban Amurka Kamala Harris sannan yayi bayani cewa, akwai wasu manyan kamfanonin Amurka masu niyyar zuba jari a kasar, don haka yana da kyakyawan zaton cewa, ziyarar Harris zata karfafawa masu niyyar zuba jari gwiwa kuma su tabbatar da cewa lallai, Ghana cibiya ce da zasu iya aiwatar da kasuwanci ba tare da sun fuskanci wata matsala ba.

Ziyarar Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris a Kasar Ghana
Ziyarar Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris a Kasar Ghana

A tattaunawarsa da wakilin Muryar Amurka Hamza Adams, mai sharhi akan tattalin arziki a Ghana Shuaib Abubkar, wanda ya bayyana cewa, ziyarar zata taimaka wa Ghana wajen shawo kan matsalalolin da take fama dasu musamman na tattalin arziki.

Ziyarar Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris a Kasar Ghana
Ziyarar Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris a Kasar Ghana

Ana sa ran cewa Uwargida Kamala Harris za ta ziyarci gidan wasan kwaikwayo inda zata gana da matasan dake masana'antar kere kere.

Ana sa ran cewa, gobe Talata ne za ta gabatar wa matasa jawabi, kuma za ta ziyarci gidan adana bayanan tarihi dake birnin Cape Coast, inda ake sa ran zata yi jawabi akan illar da safarar bayi ta yi wa nahiyar Afirka.

Sausari rahoton Hamza Adams cikin sauti:

ZIYARAR KAMALA HARRIS AGHANA.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

XS
SM
MD
LG